Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Kamar yadda ya fada a babban Taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 76 a ranar 21 ga wata, Mista Erdogan, ya ce Turkiyya za ta ci gaba da siyan makaman kariya daga makamai masu linzami kirar S-400 na Rasha, duk da tsananin adawa da hakan da Amurka ta ke yi.
Moscow da Ankara sun rattaba hannu kan yarjejeniya a 2017 don mika makamman ga Turkiyya, wacce ke zaman memba a kungiyar tsaro ta NATO.
Shi ne karon farko da wata kasa mamba a kungiyar ta sayi irin wadanan makaman daga Rasha, lamarin da ya haifar da cece kuce tsakanin mambobin kungiyar ta NATO.
Kan hakan kuma Amurka, ta sanya takunkumi kan kasar ta Turkiyya.
Ta kuma soke shirin sayar wa da Turkiyya jiragen yaki kirar F-35.
342/