Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mohammad Islami yana fadar haka a lokacinmda yake jawabi a babban taron hukumar IAEA karo na 65 a birnin Vienna na kasar Austria a jiya Litini.
Mohammad Islami ya kara da cewa, duk tare da kudurori masu yawa wadanda hukumar IAEA ta samar na haramta kai hari kan cibiyoyin Nukliya a duniya, amma hukumar ta na yin shiri kan hare-haren da ake kaiwa cibiyoyin Nukliya a kasar Iran, wannan hakan ya sa wadanda suke kai wadannan hare-hare su ke ci gaba da kai hare-hare.
Islami ya yi kira ga hukumar IAEA da ta kula da wannan bangaren don tabbatar da tsaro a shirin nukliyar kasar Iran na zaman lafiya.
Banda haka ya yi kira ga hukumar IAEA da ta taimakawa kasashe mambobi a kungiyar da fasahar da ta samu a bangaren ilmin makamashin nukliya kamar yadda yake a cikin manufofin kafa hukumar.
A cikin watan Afrilun da ya gabata ne aka kaiwa cibiyar Nukliyar kasar Iran da ke Natanz, wanda HKI ta dauki alhakin kaiwa.
342/