15 Satumba 2021 - 11:30
Binciken Kisan Shugaban Haiti, Jovenel Moïse, Ya Haifar Da Rudani

Firaministan Haiti, Ariel Henry, ya kori babban mai shigar da kara na kasar, sa’o’I kadan bayan da ya bukaci a binciki firaministan kasar kan kisan shugaba Jovenel Moïse.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Babban mai shigar da kara na gwamnatin Port-au-Prince, Bed-Ford Claude, ya zargi firaministan da yin waya da daya daga cikin ‘wadanda ake nema ruwa a jallo kan kisan tsohon shugaban kasar Jovenel Moïse.

Mista Claude, ya bukaci lauyen dake bincike kan kisan shugaba Jovenel Moïse, da ya gurfanar da firaministan kasar.

Hakan ne ya sa firaministan kasar ya sanar da korar babban mai shigar da kara na kasar, kan abunda ya kira aikata babban kuskure kan aiki, kuma tuni ya maye gurbisa.

Kawo yanzu dai binciken da ake kan kisan shugaba Moise, ya haifar da wani sabon rikicin cikin gida a wannan kasa mafi talauci a yankin Amurka.

To saidai kodin tsarin mulkin kasar na 1987, ya tanadi cewa shugaban kasar ne kawai ya ke da nauyin kora ko kuma nada babban mai shigar da kara na kasar.

342/