Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Kamfanin dillancin labaran Sabirun ya bayyana haka a cikin shafinsa na Telegram a safiyar yau Lahadi, ya kuma kara da cewa mai yuwa yawan wadanda suka rasa rayukansu ya karu, saboda raunuka masu tsanani da aka yiwa wasu jami’an tsaron.
Banda haka an budewa juna wuta bayan wannan harin tsakanin ‘yan ta’addan da kuma jami’an tsaron na kasar ta Iraki.
Tun shekara ta 2017 ne aka kawo karshen mamayar da kungiyar Daesh ta yiwa arewacin kasar Iraki, da kuma abinda da kira daula Isalamiyya, amma har yanzun akwai ragowarsu da suke kai hare-hare kan mutane da kuma jami’an tsaron kasar, har’ila yau da kuma kan sandunan wutan lantarki na kasar daga lokaci zuwa lokaci.
342/