Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Harin da yan bindigan suka kai makarantar ta NDA sun kashe manyan sojoji 2 tare kuma da yin garkuwa da major Detong , rahotanni sun nuna cewa da farko yan bindiga dake sanya da kakin soji sun yi wa masu gadin kofar shiga kwalejin dukan tsiya kafin su kutsa kai zuwa rukunin gidajen da manyan sojoji yake a ciki,
Ita dai wannan kwalejin ta NDA tana daura ne da kwallejin koyar da ayyukan Noma da gandun daji dake garin Afaka wanda a ranar 11 ga watan Maris yan bindiga suka kutsa kai su ka yi a won gaba da dalibai 39 , wanda bayan kwanaki suka neman a basu kudin fansa har N miliyan 500 kafin su sako su,
342/