Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA : Baradar na cikin manyan shugabannin Taliban da suka dawo gida a ranar Talata.
Sun dawo ne daga Qatar zuwa Kandahar, tushen Taliban.
Baradar na cikin wadanda suka assasa Taliban, kuma yana cikin shugabannin da ke jagorantar tattaunawa da Amurka a Qatar bayan sakinsa daga gidan yari domin taimakawa ga tattaunawar sulhu.
A 2010 aka kama shi a wani samamen dakarun Amurka a Karachi.
Ana kallon wannan a mastayin wani yunkuri da wannnan kungiyar ke yi na kara karfin ikonta tun bayan data kwace mulkin kasar ta Afghanistan.
342/