Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayya cewa tashar jiragen sama na Kabul ta cika da mutane wadanda suke son ficewa daga kasar bayan da mayakan Taliban suka shiga birnin Kabul, sannan sojojin Amurka kimani 5000 da suke wurin suna kokarin kwasar jami’an diblomasiyyar kasar zuwa waje daga ciki har da jakadan kasar ta Amurka a Kabul Mr Ross Wilson.
Wadanda suka ganewa idanunsu sun bayyana cewa sojojin Amurka sun bude wuta a sama don tarwatsa cicirindon mutane dasuka cika tashar jiragen saman a kokarinsu na samun jirgi na karshe wanda zai fata daga kasar.
Sai dai shuwagabannin tashar jiragen saman sun fadawa ‘yan kafafen yada labarai kan cewa iko tashar jiragen saman da kuma harkokin sararin samnaiyar kasar Afganistan tuni sun koma hannun kungiyar ta Taliban.
Har’ila yau a wani labarin kuma mayakan Taliban sun fara karban makamai daga hannun mutane a birnin Kabul babban birnin kasar saboda tsohon tashin hankali nan gaba a kasar.
342/