30 Yuli 2021 - 14:08
Iran Ta Soki Kwamitin Tsaro Kan Kin Daukar Mataki Game Da Cin Zarafin Da Isra’ila Ke Wa Falasdinawa

Iran, ta soki kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, game da kasa daukar wani mataki kan cin zarafin da Isra’ila ke ci gaba da yi wa al’ummar Falasdinu.

ABNA24 : Da take sanar da hakan, mataimakiyar wakilin dindindin na Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Zahra Ershadi, ta ce "Tsawon shekaru da yawa na rashin daukar mataki daga MDD, hakan ya kara karfafawa gwamnatin sahayoniya ci gaba da aikata muggan laifuka a gabas ta tsakiya musamman kan al’ummar Falasdinu.

A daya bangaren kuma jami’ar, ta caccaki Amurka saboda yadda take karfafawa Isra’ila ta hanyar hawa kujerar na ki, game da duk wani kudiri da aka gabatar a kwamitin Tsaron MDD.

Zahra Ershadi, ta kawo misalign, matakin da Amurka ta dauka, a cikin watan Mayun 2021, na hana Kwamitin Tsaro fitar kudiri na kawo karshen harin da Isra'ila ta kai Gaza."

342/