ABNA24 : Jaridar Leadership ta Najeriya ta nakalto kamfanin ya na cewa a cikin watan da ya gabata ne gwamnatocin kasashen biyu suka kaddamar da aikin, wanda zai lakume dalar Amurka biliyon $7, sannan tsawon bututun zai kai kilomita 1,980.
Labarin ya kara da cewa ana saran aikin zai kammala a shekara ta 2024, sannan yawan danyen man fetur wanda kasar Niger za ta haka a ko wace rana zai tashi daga ganga 20,000 zuwa 120,000.
Kafin haka dai gwamnatin Nigeria ta fara tattaunawa da gwamnatin kasar Niger da kuma kamfanin man fetur na kasar ta Cana don shimfida bututun a cikin Nigeriya. Amma da alamun Najeriya ta rasa wannan damar.
342/