ABNA24 : Kana Mista Tedros ya bayyana cewa, ya kamata kamfanin Pfizer, da na Moderna, wadanda ke samar da alluran rigakafin cutar COVID-19, su samar da alluransu ga shirin COVAX, maimakon samar da allurai ga kasashen da yawancin jama’ar su, sun riga sun karbi alluran rigakafin.
Wannan kiran na hukumar ta WHO, na zuwa ne a daidai lokacin da ake sake tinkarar yanayi mai tsanani na yaduwar cutar COVID-19 a duniya.
Nau’in cutar na Delta shi ne dai yanzu haka ke yaduwa cikin sauri a kasashen duniya, yayin da tuni wasu kasashe suka fara hasashen yi wa jama’arsu allurar ta korona a karo na uku a yayin da wasu kasashen musamman marasa galiho suka zama ‘yan kallo.
342/