ABNA24 : Rahotanni daga ƙasar Afirka ta Kudun sun ce da tsakar daren jiyan ne daf da wa’adin da aka ba shi na ya miƙa kansa ga ‘yan sandan ne tsohon shugaba Zuman ya bar gidansa bisa rakiyar ‘yan sanda zuwa gidan yarin da ke KwaZulu Natal don fara zaman gudan yarin da aka yanke masa na watanni sha biyar saboda ƙin girmama umurnin kotu da yayi.
Bin umurnin kotun da Mr. Zuma yayi ta hanyar miƙa kansa ga gidan yarin, bayan kwanaki na nuna alamun taurin kai da yayi, ya kawo ƙarshen ce-ce-ku-cen da ake ta yi a ƙasar da kuma wani tsaka mai wuya na siyasa da ƙasar Afirka ta Kudun ta shiga sakamakon wannan lamarin.
A ranar 29 ga watan Yunin da ya gabata ne dai kotun tsarin mulki na Afirka ta Kudun ta ɗaure Mr. Jacob Zuma, wanda ya mulki Afirka ta Kudun daga shekara ta 2009 zuwa 2018, tsawon watanni goma sha biyar a gidan yari saboda rashin biyayyar da yayi ga wani umurni da aka yi masa na ya ba da shaida cikin bincike da ake gudanar bisa zargin gagarumar rashawa da cin hanci da ake yi wa gwamnatinsa.
Bayan wannan hukuncin dai Zuman ya ƙi amincewa da hukuncin kamar yadda magoya bayansa kuma suka ta nuna bijirewa da kuma sanar da cewa ba za su bari a tafi da shi ba, lamarin da ya sanya kotun ba wa ‘yan sanda umurnin kamo shi matuƙar bai miƙa kansa kafin wa’adin tsadar daren jiya Laraba da kotun ta tsayar ba.
A halin yanzu dai mahukunta sun ce za a killace shugaba Zuman a gidan yarin har na tsawon makonni biyu don kula da dokokin kariya na cutar COVID-19, kamar yadda suka ce akwai yiyuwar a yi masa afuwa bayan watanni huɗu.
Wannan dai shi ne karon farko da aka taɓa ɗaure wani tsohon shugaban ƙasa a Afirka ta Kudun.
342/