6 Yuli 2021 - 13:36
Iraki:Sojojin Kasar, ‘Yan sanda Da Kuma Hashdu Zasu Ci Gaba Da Kare Cibiyoyi Da Kayakin Lantarki Na Kasar Daga Daesh

Hadin guiwar jami’an tsaron kasar Iraki wadanda suka hada da Sojoji, ‘Yansanda, da kuma Hashdu sun samar da wata runduna ta musamman don kare cibiyoyin bada wutan lantarki a kasar daga hare-haren mayakan kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Manjo Janar Tahsin Alkhaffaji kakakin rundunar hadin guiwar yana fadawa kamfanin dillancin labaran INA na kasar Iraki a safiyar yau Litinin.

Alkhaffaji ya bayyana cewa mayakan kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh sun kai hare-hare kan cibiyoyin bada wutan lantarki kimani 45 a cikin kasar Iraki a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata.

Ma’aikatar wutan lantarki ta kasar Iraki ta bayyana cewa a makon da ya gabata mayakan Daesh sun wargaza cibiyar bada wutan lantarki na Lardan Sahahuddeen da makaman katusha, wanda ya haddasa katsewar wutan lantarki a lardin.

342/