ABNA24 : Majiyoyin sojin sun bayyana wa kamfanin dillancin labaran Reuters jirgin wanda na ɗiban kaya ne samfurin Lockheed C-130 yana ɗauke ne da fasinjoji 96 da ake shirin kai su aikin faɗa da masu tada ƙayar baya a ƙasar inda yayi hatsari a yankin Patukul da ke lardin Sulu na ƙasar.
Tun da fari dai majiyar sojin ta ce baya ga waɗanda suka mutun har ila yau kuma wasu mutum 50 sun jikkata sannan wasu 17 kuma ba gan su ba, kamar yadda waɗanda suka tsira kuma an kai wani asibitin sojoji don yi musui magani.
Majiyar sojin ta ƙara da cewa lamarin ya faru ne lokacin da jirgin yake shirin sauka lokacin da ya zarce titinsa. Sojojin dai sun kore yiyuwar kai wa jirgin hari.
Sjojin na Philiphines dai sun jima suna yaƙi da dakarun ƙungiyar Abu Sayyaf da sauran ƙungiyoyi masu ikirarin jihadi waɗanda suke da alaƙa da ƙungiyar ta’addancin nan ta Al-Кa’ida da sauransu.
342/