ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press (IP) ya nakalto ministan kiwon lafiya na kasar Saeed Namaki ya na bada wannan sanarwan a jiya Talata.
Wannan dai ita ce alluran riga kafin cutar korona na biyu wacce ta sami lasisin amfani da ita a cikin kasar Iran.
Ministan ya kara da cewa an kammala dukkan ayyukan gwaje-gwajen alluran riga kafin a dukkanin marhalolin gwajinta, daga ciki har da gwaji kan mutane 44,000 a kasar Cuba da kuma wasu 25,000 a kasar Iran.
Ministan ya kammala da cewa kwararo a hukumar abinci da magunguna sun tabbatar da ingancin alluran, wanda ya sa aka sanya ta cikin jerin alluran riga kafin cutar korona wadanda za’a yi amfani da su a cikin gida.
342/