20 Yuni 2021 - 11:57
​Ghana: An Gudanar Da Zaman Taron Shugabannin Kasashen ECOWAS

A jiya Asabar ne shugabannin kasashe mambobi a kungiyar ECOWAS sun gudanar da zaman taronsu na tsakiyar shekara a birnin Accra na kasar Ghana.

ABNA24 : A yayin zaman na jiya dai an tattauna batutuwa daban-daban da suke a cikin ajendar taron, amma abubuwan da suka fi mamaye taron dai su ne batun halin da ake ciki a kasar Mali, sai kuma batun samar kudi na bai daya a tsakanin kasashen yammacin nahiyar Afirka.

Baya ga haka kuma taron ya yi dubi kan batun matsalar cutar corona, da kuma irin matakan da ake dauka wajen dakile cutar a cikin kasashe mambobi a kungiyar ECOWAS.

Haka nan kuma taron ya duba batun shirin nan na bunkasa harkokin kasuwanci da cinikayya tsakanin kasashen Afirka, tare da samar da yankunan hada-hadar kasuwanci da ba a karbar haraji a tsakanin kasashen Afirka.

Sai kuma batun tsaro da yaki da ta’addanci da ya addabi wasu daga cikin kasashen yammacin nahiyar Afirka, da yadda dukaknin kasashen za su yi aiki tare wajen tunkarar wannan barazana ta tsaro.

A yayin zaman ne kuma manzon musamman na kungiyar ECOWAS a kan rikicin kasar Mali, kuma tsohon shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan, ya gabatar da rahoton da tawagarsa ta harhada dangane da halin da ake ciki a kasar ta Mali, tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar.

342/