19 Yuni 2021 - 19:11
Ghana Na Karbar Taron Shugabannin ECOWAS Karo Na 59

Yau Asabar, shugabannin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS, na halartar wani taron kungiyar karo na 59 a birnin Accra na kasar Ghana.

ABNA24 : Mali dai ba ta daga cikin kasashen dake halartar taron bayan dakatar da ita saboda juyin mulkin da sojoji sukayi har sau biyu a cikin wata tara.

Saidai ana sa ran tsohon shugaban Najeriya kuma manzo na musamman a kungiyar ECOWAS da ke sasanta rikicin kasar Mali Goodluck Jonathan zai gabatar da rahotonsa ga shugabannin kasashen kungiyar kan ziyarar da ya kai kasar Mali kwanakin baya.

Kazalika shugabannin kasashen kungiyar za su karbi rahoto kan sauye-sayen da za a yi a tsarin ECOWAS, ciki har da shirinta na samar da kudin bai-daya da kuma batun karba-karbar da kasashen kungiyar za su yi a takarar shugabancin kungiyar Kasashen Afirka wato AU.

342/