ABNA24 : A jiya Jum’a ne bangarorin suka sanar da cimma wata yarjejeniya inda Isra’ila za ta baiwa Falasdinawan alluran riga kafin korona miliyan daya samfanin Pfizer.
Saidai daga bisani Falasdinun ta yi watsi da yarjejeniyar tana mai cewa lokacin amfani da riga kafin na daf da kawo karshe.
Hukumomin Falasdinawan sun ce bayan gwajin kashin farko na rigakafin da aka karba daga Isra’ila, an gano cewa bai tafiya daidai da yarjejeniyar da aka cimma, don haka gwamnatin Falasdinun ba zata karbi riga kafin ba da wa’adin aikinsa ke daf da kawo karshe.
Yanzu haka dai Falasdinun ta ce tana kan mayar wa da Israilaalluran 90,000 data riga ta karba ba.
Falasdinu ba ta bayyana takamaimai yaushe ne riga kafin da Isra’ilar ta ba ta zai kawo karshe ba.
Dama dai kafin hakan Falasdinawa da dama sun soki yarjejeniyar karbar alluran daga Isra’ila.
342/