ABNA24 : Gwamnatin kasar ta sake fito da wasu tsauraran maatakai domin dakile yaduwar cutar.
Shugaban kasar Felix Tshisekedi ya kara da cewa; Yanayin da ake ciki dangane da annobar Covid ya yi tsanani, muna ganin yadda ake kara samun masu kamuwa da ita da ya hada da asarar rayuka.”
A ranar juma’ar da ta gabata an sami rasuwar mutane uku da kuma wasu 254 da suka kamu da cutar, daga cikinsu da akwai 210 a cikin birnin Kinshasa.
Shugaban kasar ta Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ya ci gaba da cewa; Saboda yadda wannan cutar take kara yaduwa, jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta yanke shawarar daga lokacin bukukuwan girmama Patrice Lumumba har zuwa watan Janairu na 2022.
342/