ABNA24 : Tashar talabijinn ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa an watsa yadda munazarar ta gudana kai tsaye ta kafafen yada labarai na gidajen talabijin da Radityo ta kasa da kuma da kuma ta yanar gizo.
Maudu’in munazarar dai shi ne ‘tsarin tattalin arzikin da ko wane dan takara yake shirin gabatarwa idan ya sami nasarar zama shugaban kasa a zabe mai zuwa’.
Har’ila yau Labarin ya kara da cewa mutane, a ciki da wajen kasar sun bada lokutansu don kallon Munazarar, da dama sun yaba da yadda ta gudana.
A mako mai zuwa ne za’a gudanar da munazara ta biyu tsakanin yan takaran guda 7.
342/