ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Annashrah na kasar ta Lebanon ya nakalto Diab ya na fadar haka a jiya Laraba, ya kuma kara da cewa, a halin yanzu kwanaki 300 kenan da saukar gwamnatinsa amma ‘yan siyasar kasar sun kasa kafa gwamnati. Sannan kasar ta na kara nutsewa cikin fatara da talauci mafi muni a tarihin kasar.
Firai ministan ya ce saukar gwamnatinsa ta tsaida tattaunawar da ta fara tare da hukumar bada lamuni ta IMF don karban bashi.
Daga karshe Diab ya kammala da cewa akwai bukatar kasashen duniya su taimaka don ganin an kafa gwamnati a kasar ta Lebanon da gaggawa.
A halin yanzu dai shugaban kasar Nichel Aun ya bawa Sa’adul Hariri na jam’iyyar Mustaqbal damar kafa gwamnati amma yau watannin 8 kenan ya kasa yin haka ya kuma ki bayyana gazawarsa na yin hakan.
342/