1 Yuni 2021 - 13:21
​ECOWAS Ta Dakatar Da Mali Saboda Juyin Mulki

Kungiyar ECOWAS ta sanar da dakatar da Mali daga jerin kasashe mambobinta yayin wani taro da shugabannin kasashen kungiyar suka gudanar jiya a Ghana, biyo bayan juyin mulkin Soji da kasar ta sheda har sau biyu cikin watanni 9.

ABNA24 : Gidan Rediyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, taron ya gudana ne a jiya bisa jagoranci shugabannin kasashe 10 da ministocin harkokin waje biyu a birnin Accra na Ghana, wanda kuma taron ya mayar da hankali ne baki daya kan halin da ake ciki a kasar Mali.

Ministan harkokin wajen Ghana, Shirley Ayorkor ya ce dakatarwar da aka yi wa Mali daga jerin kasashen na ECOWAS ya fara aiki ne nan take daga jiya Lahadi 30 ga watan Mayu har zuwa watan Fabarairun 2022 lokacin da aka tsara Sojin za su mika mulki ga zababben shugaban farar hula.

Taron na ECOWAS wanda ya samu halartar masu shiga tsakani a rikicin siyasar Malin karkashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya karkare da bukatar ganin lallai kasar ta tabbatar da nadin farar hula a matsayin jagoran gwamnati.

Haka zalika sanarwar da ECOWAS ta fitar bayan taron ta nuna cewa, ba za a amince shugaban gwamnatin Sojin kasar da mataimakinsa da ma Firaministansa su iya samun damar tsayawa takara a zaben da aka tsara gudanarwa a kasar domin mika mulki ga fararen hula karkashin demokradiyya ba.

342/