1 Yuni 2021 - 13:19
​Vienna:Araqchi Ya Ce Bai Da Tabbas Ko Wannan Shi Ne Taron Vienna Kan JCPOA Na Karshe

Babban mai jagorantar tawagar tattaunawa dangane da shirin nukliyar kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa bai da tabbacin cewa taron Vienna na yanzu shi ne taro na karshe dangane da shirin nukliyar kasar ba.

ABNA24 : Araqchi ya bayyana cewa an cimma matsaya kan wasu al-amura masu muhimmanci da dama, amma har yanzun akwai bututuwa masu muhimmanci wadanda tattaunawar ta cije a kansu.

Amurka ta fice daga yarjejeniyar JCPOA a shekara ta 2018 da tufin samar da sabuwar yarjejeniya. Shugaba Biden ya ce zai dawo cikinta, amma Iran ta kafa mata sharuddan dawowarta cikin yarjejeniyar, daga ciki har ba dage mata dukkan takunkuma tattalin arzikin da ta dora mata, sannan ta bata lokaci don tabbatar da cewa an dage su kafin ta dawo.

342/