ABNA24 : Har ila yau Huthi ya shaidawa dan sakon na MDD, cewa; Batun ayyukan agaji su ne mabudin warware dukkanin batutuwan da ake Magana akansu, domin hakan ya shafi rayuwar al’ummar kasar kai tsaye.
A farkon wannan watan ne dai manzon na MDD, ya kai ziyarar aiki zuwa kasashen Saudiyya da Oman, a kokarin gano bakin zaren yadda za a warware matsalar da kasar Yemen din take ciki.
Ziyarar ta Griffth zuwa kasar Yemen tana a karkashin kokarin da ake yi ne na samar da yadda za a tsagaita wutar yaki.
342/