31 Mayu 2021 - 12:53
​Iran : Kwamitin Zabe Ya Shirya Tsaf Domin Gudanar Da Zabe A Ketare

Shugaban kwamitin zabe a nan kasar Iran ya bayyana cewa kwamitinsa ya kammala shiri don gudanar da zaben shugaban kasa ga Iraniyawa mazauna kasashen waje.

ABNA24 : Majiyar muryar jumhuriyar Musulunci ta Iran ta nakalto Jamal Urf ya na fadar haka a safiyar Lahadi, ya kuma kara da cewa, a wannan fagen kwamitinsa ya na aiki tare da ma’aikatar harkokin wajen kasar don ganin an tara kuriun masu zabe a ofisoshin jakadancin kasar, daga Iraniyawa mazauna kasashen waje.

Labarin ya kammala da cewa shirye-shirye don hakan ya kammala tare da taimakon ma’aikatar harkokin wajen kasar.

Har’ila yau Sayyid Kazin Sajjadi, jami’iin mai kula da al-amuran harkokin waje a majalisar dokokin kasar ya ce, sun samar da akwatunan zabe a garuruwan da ke da iraniyawa da yawa a wasu kasashen, ta yadda ba sai sun zo babban birnin kasar don kaka kuri’arsu ba.

Za’a gudanar da zaben shugaban kasa karo 13 a nan kasar Iran ne a ranar 18 ga watan Yuni da muke ciki a duk fadin kasar da kuma kasashen waje.

342/