27 Mayu 2021 - 12:55
Mali : Sojojin Sun Saki Shugaba Da Firaministan Rikon Kwarya

Rahotanni daga Mali, na cewa sojoji sun saki shugaba da firaministan rikon kwarya da sukayi murabus.A ranar Litini data gabata ne sojojin suka tisa keyar shugaban rikon kwarya na kasar Bah N’Daw, da firaministansa Moctar Ouane, zuwa barikin sojin Kati, kafin daga bisani su sanar da yin murabus a jiya.

ABNA24 : Dama dai kafin hakan, mataimaki shugaban rikon kwaryar soji na kasar kana kuma tsohon shugaban kwamitin ceton al’ummar kasa (CNSP) Assimi Goita, Ya shaidawa taron manema labarani cewa, za a saki shugaban rikon kwarya da firaministan, bayan da suka ajiye mukaman nasu.

Tunda farko dai an tabbatar da cewa, N’Daw da Ouane, sun mika takardunsu na yin murabus a gaban mai shiga tsakani na kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) Goodluck Jonathan. Ya kuma gaskata kame jami’an biyu, kan abin da ya kira “bambanci ra’ayi dake tsakaninsu, kan tsari da abubuwan da suka shafi mika mulki.”

342/