ABNA24 : Majiyar muryar jumhuriyar musulunci ta Iran ta nakalto Mohammad Hassan Mukaddam shugaban kungiyar ya na fadar haka a safiyar yau Talata.
Ya kuma kara da cewa ya zuwa yanzun kungiyarsa ta shigo da alluran riga kafin cutar korona har miliyon 2.5. Sannan ta na da shirin shigo da akalla alluran riga kafin cutar har miliyon 10 nan gaba.
Mukaddam ya kara da cewa kungiyarsa ta na hulda da kawayenta a kasashe 192 na duniya don samar da kudaden sayan alluroran daga wuraren daban-daban a duniya.
342/