ABNA24 : ‘yan adawan sun ce sharudan da kwamitin tsaron kungiyar ya gindaya wa sojojin bai isa ba, kamata ya yi a dau matakin takunkumi kan sojojin saboda karbar mulki ta haramtacciyar hanya.
A nata bangare majalisar sojojin ta ce ta ji dadin yadda kungiyar tarrayar Afrika ta dauki batun Chadi da mahimmanci, kuma za’a warware sauren sabanin dake akwai ta hanyar taron kasa da zai hada dukkan bangarorin ‘yan siyasa na kasar.
Kungiyar ta AU, ta bukaci majalisar sojojin kasar ta Chadi, data mika mulki bisa tsarin demokuradiyya cikin watanni 18.
Majalisat ta CNT, da dan Idriss Deby Itno ke jagoranta, ta karbi mulki ne a ranar 20 ga watan Afrilu, bayan ta sanar da rasuwar shugaba Deby, wanda ya mutu a fagen daga a yaki da ‘yan tawaye.
342/