ABNA24 : WHO, ta sanar a jiya Juma’a cewa, allurar rigakafin cutar COVID-19 na kamfanin Sinopharm na Sin, ta samu izinin hukumar na amfani da ita a matakin gaggawa.
Hakan ya sa allurar Sinopharm ta zama irinta ta 6 da ta samu izinin WHO, kuma allura daya tilo ta kasar da ba ta yammacin duniya ba.
Shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana yayin wani taron manema labarai cewa, wannan mataki zai taimaka wajen habaka allurar da shirin COVAX zai saya a duniya, kuma zai karfafa gwiwar kasashen duniya wajen gaggauta amincewa da allurar don amfani da ita a kasashensu.
342/