5 Mayu 2021 - 14:37
An Bude Taron Kasa Da Kasa Akan Quds Ta Hanyar Bidiyo Daga Nesa Daga Nan Iran

Taron akan birnin Kudus ta hanyar bidiyo daga nesa, shi ne irinsa na biyu, saboda bullar cutar corona, kuma baki ne daga cikin gida da waje za su yi bayanai domin raya ranar Kudus ta duniya. Bakin za su yi jawabai a cikin harsunan Farsi, turancin Ingilishi, da kuma Larabci.

ABNA24 : Daga cikin jigo-jigo da za a tattauna da akwai batun kare hakkin dan’adam,mamayar da ‘yan sahayoniya su ka yi wa birnin Kudus mai tsarki da kuma kudurorin da MDD ta fitar akan wannan birnin.

Masu gabatar da jawabai sun kai 30 daga kasashen Iran, Palasdinu, Malaysia, India, Pakistan, Fransa, Argentina, Iraqi. Sai kuma Turkiya, HDL, Lebanon, Syria, UK, Canada da Tunisiya.

Musulmi a ko’ina a duniya suna raya juma’ar karshe ta kowance azumin watan Ramadan a matsayin ranar Kudus, bisa umarnin marigayi Imam Khumain ( r.a) tun bayan cin nasarar juyin juya halin musulunci a Iran.

342/