29 Afirilu 2021 - 14:02
Najeriya : INEC Ta Tsayar Da Ranar Babban Zaben 2023

Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC, a Najeriya, ta tsaida ranar 18 ga watan Fabrairun 2023, a matsayin ranar da za’a gudanar da babban zaben kasar.

ABNA24 : Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan jiya Laraba.

Hakan dai na nufin ya rage saura shekara guda da wata Tara kafin a je babban zaben na 2023 idan fa Allah ya kai.

Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi hasashen cewa yawan masu rajistar zabe a Najeriyar za su iya kai miliyan 100 kafin babban zaben 2023.

Shugaban na INEC wanda ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da hukumomin kasashen waje da suka hada da hukumar raya kasa ta Amurka USAID a Abuja ya ce za a ci gaba da yin rijistar masu zabe daga 28 ga watan Yunin bana har zuwa karshen 2022.

342/