ABNA24 : Takwarorinsu na kungiyar G5 Sahel ne suka dora masu wannan nauyin domin tattaunawa da ‘yan siyasar kasar a wani mataki na sansanta rikicin siyasar da ya kunno kai bayan mutuwar tsohon shugaban kasar mirigayi Idriss Deby Itno.
Masu shiga tsakanin wato Mohammed Bazoum na Nijar da kuma takwaransa na Mauritania, Mohamed Ould Ghazaoui, zasu tattaunawa da ‘yan siyasar na Chadi, kan irin salon mulkin rikon kwarya da suke bukata.
An dau wannan matakin ne duba da cewa har yanzu kungiyar kasashen tsakiyar Afrika bata dau wani mataki ba, a cewar shugabannin biyu da aka nada domin shiga tsakanin rikicin Chadin.
Sabanin dake akwai tsakanin ‘yan siyasar kasar ta Chadi, shi ne nadin da akayi wa dan mirigayin cewa da Janar Mahamat Idriss Deby, a matsayin shugaban kwamitin rikon kwarya na sojoji, da zai mulki kasar na tsawon watanni 18.
A jiya dai shugabannin biyu sun tattauna da ‘yan siyasar kasar ta Chadi, a N’Djamena, yayin da suka halarci jana’izar tsohon shugaban kasar ta Chadi, wanda aka sanar da rasuwarsa a ranar Talata data gabata, sakamakon samun raunin da ya yi a fagen daga a yaki da ‘yan tawayen kasar na FACT a arewacin kasar.
342/