12 Afirilu 2021 - 12:24
A Kalla Mutane Uku Ne Su Ka Mutu Sanadiyyar Harin Kumar Bakin Waje A Kasar Somaliya

Majiyar tsaron kasar ta Somaliya ta ce; Daya daga cikin gwamnonin kasar ya tsallake rijiya da baya sanadiyyar harin kunar bakin da aka kai masa,amma mutane uku sun mutu, biyu masu tsaron gwamnan. Har ila yau, wasu mutane biyu na daban sun jikkata.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labarun “Anadoula” ya bayar da labarin da ke cewa; Wan dan kunar bakin wake ya tarwatsa kasan a bakin wani hotel da ke birnin Baidoa, babban birnin gundumar kudu maso yamma.An kuwa kai harin ne akan gwamnan gundumar Ali Wardhere Dooyow.

Babu abinda ya sami gwmanan amma biyu daga cikin masu tsaronsa sun mutu sai kuma wani mutum guda na daban.

Jami’in ‘yansanda a Bidouwa Muhammad Adan Ibrahim ya fada wa manema labaru cewa; Mafi yawancin mutane biyar din da su ka jikkata fararen hula ne , kuma tun an dauke su zuwa asibiti.

Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta sanar da kai harin, amma jamian tsaron kasar suna zargi al-Shabab da hannu.

342/