ABNA24 : Mista, Zarif, ya bayyana hakan ne yayin tattaunawar da ya yi da takwaransa na Biritaniya ranar Asabar, kan tattaunawar da ake sa ran yi a birnin Vienna, a wani mataki na farfado da yarjejeniyar bayan ficewar Amurka yau da shekaru uku.
A ranar Talata mai zuwa ce kwamitin hadaka na kasashen da suka hada da Iran, Faransa, Biritaniya, Jamus, Rasha da kuma China zasu hadu a birnin Vienne domin tattaunawa kan makomar yarjejeniyar, karon farko bayan zuwan gwamnatin shugaba Joe Biden na Amurka.
Yarjejeniyar dai ta 2015, ta rasa makoma ne tun bayan da gwamnatin AMurka, karkashin tsahuwar gwamnatin Donald Trump, ta fice daga cikinta tare da kakaba wa Iran takunkuman karya tattalin arziki, lamarin daya tilastawa ita ma a nata bangare Iran daukar mataki na dakatar da aiki da wasu bangarori da yarjejeniyar ta kunsa a matsayin maida martani.
Saidai Iran ta ce a wannan tattaunawar, ba wai yana nufin ta bude tattaunawa ne ba da Amurka, tana nan kan bakarta har sai Amurkar ta dage mata gabadayen takukuman data dora mata a lokaci guda kafin ta dakatar da matakan data dauka.
342/