ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto Faisal bin Farhan yana fadar haka a hirar da ta hada shi da tashar talabijin ta CNN ta kasar Amurka a jiya. Farhan yana kara da cewa, Saudia da sauran kasashen yankin za su mafani da HKI ta bangarorin tsaro, tattalin arziki da kuma zamantake idan sun samar da hulda da haramtacciyar kasar.
Har’ila yau ministan ya kara da cewa gwamnatin kasar Saudia za ta bada izinin shiga kasar Saudia ga dukkan mazauna HKI da ga ko wani addini suke.
A wani bangaren Faisal bin Farhan ya kaucewa tambaya, dangane da hukunta jami’an gwamnatin kasar wadanda suka kashe Jamal Kashaggi, da cewa akwai dangantaka mai karfi tsakanin Saudia da Amurka.
342/