2 Afirilu 2021 - 19:40
Rauhani: Wajibi Ne A Kare Tsarin “ Jamhuriyar Musulunci” Ta Kowane Hali

Shugaban Kasar Iran Dr. Hassan Rauhani wanda ya yi Magana a ranar; jamhuriyar musulunci” wacce take kamawa a kowace ranar 1 ga watan Aprilu, ya kara da cewa; Wajibi ne a kiyaye bangarori uku na wannan tsarin, wadanda su ne; Jamhuriya, ‘musulunci”, da kuma kasantuwarta a Iran.

ABNA24 : Shugaban kasar ta Iran ya kaddamar da manyan ayyuka na kasa wanda yake a karkashin sunan da aka bai wa shekarar bana na bunkasa ayyukan kere-kere da ci gaba a cikin kasa.

Dr. Hassan Rauhani ya ci gaba da cewa; Gwamanti za ta ci gaba da gudanar da manyan ayyuka na raya kasa da ci gabanta ta hanyar tallafawa al’umma, da aiki tare a tsakanin hukuma da kamfanoni masu zaman kansu da kuma ‘yan kasuwa.

Shugaban kasar ta Iran ya kuma ce; Har yanzu makiya ba su fahimci hakikanin azamar al’ummar Iran ba da kuma ita kanta wannan kasa mai girma.

342/