ABNA24 : Rahotanni daga Libiyar, sun ce an harbe Al-Warfalli da bindiga a birnin Benghazi.
A shekarar 2017 ne Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta duniya ta zargi Warfalli da aikata laifukan yaki bayan kashe mutane 33 a yankunan Benghazi daban-daban, sannan ya kuma sanya aka kashe wasu mutane 6 ba tare da yi musu shari'a ba.
A watan Satumban 2020 Tarayyar Turai ta sakawa Warfalli da wasu mutane 2 takunkumi sakamakon keta hakkokin dan adam a Libiya.
A baya, an ga yadda Warfalli da magoya bayansa suka din ga kashe fararen hula a Libiya.
342/