ABNA24 : Ministan harkokin wajen na Iran ya taya al’ummar Iran mazauna kasashen waje da kuma dukkanin masu Magana da harshen farisanci a duniya murnar zagayowar “Noroz”.
Muhammad Jawad Zarif ya bayyana shekarar da ta wuce da cewa tana cike da kalubale ga Iran da wasu kasashe masu yawa a duniya.
“ Ci gaba da barazanar da cutar corona take yi ga duniya, ya sake tabbatar wa al’ummar duniya cewa hatta manyan kasashe suna fuskantar gagarumin kalubale daga kwayar cutar da ba a iya gani da ido, wacce a yanzu ta zama wata cuta da dukkanin mutane su ke fukanta” kamar yadda Zarif ya bayyana.
Muhammad Jawad Zarif ya kuma ce; Lokaci ne da al’ummar Iran za su kara hakuri da juriya da kuma tsayin daka da sadaukar da kai domin samun galaba akan cutar Covid-19.
A karshe Zarif ya nemi gafarar al’ummar Iran a duk inda gwamnati ta gaza, amma abinda gwamnati ta sa a gaba shi ne daukaka mutunci da martabar Iran.
342/