17 Maris 2021 - 13:02
Shugabar Hukumar WTO, Ta Gana Da Shugaba Buhari Na Najeriya

A ci gaba da ziyarar da ta ke a Najeriya, sabuwar shugabar Hukumar cinikayya ta duniya, Ngozi Okonjo-Iweala, ta gana da shugaba Buhari na Najeriya a jiya Litini.

ABNA24 : Madam Ngozi Okonjo-Iwela ta ce taimako da goyon bayan da shugaban kasarta Najeriya Muhammadu Buhari ya yi mata ne ya bata damar samun nasarar hawa kujerar jagorancin hukumar ta WTO.

A nasa bangare, shugaba Buhari ya ce duk da goyan bayan da gwamnatinsa ta bata, Ngozi Okonjo-Iweala na da kwarewar da ake bukata na jagorancin hukumar.

Buhari ya ta ya Okonjo-Iwela murna tare da yi mata fatar alheri wajen sauke nauyin da ke kan ta.

Hukumar dai ta (WTO) ta yi alkawarin yin aiki a matsayin wata cibiyar raya tattalin arziki da sauran cibiyoyin dake shafar al’amurran kudade domin tallafawa Najeriya a fannin zuba jari da taimakon kwararru domin rage matsalolin tattalin arziki ga Najeriyar.

342/