ABNA24 : An gudanar da wani biki a hedkwatar gwamnatin kasar dake birnin Tripoli, jiya Talata, inda sabon shugaban kasar Mohammed Menfi ya yaba da yadda aka mika mulkin lami lafiya.
Mohammed Menfi, ya kuma tabbatar da cewa, babban aikin dake gaban sabuwar gwamnatin shi ne, shirya zaben dake tafe, yana mai cewa za a mika mulki ga duk wanda aka zaba.
Firaministan gwamnati mai barin gado da MDD ke marawa baya, Fayez Serraj, ya jaddada bukatar yin sulhu a kasar.
Shi kuwa sabon firaminista Abdul Hamid Dbeibah, ya tabbatar da cewa, gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen gudanar da gyare-gyare a kasar, yana mai kira ga hukumomin gwamnati su shiga a dama da su wajen magance matsalolin da al’umma ke fuskanta.
342/