ABNA24 : Sai dai Iraqchi ya kara da cewa; Hakan ba ya nufin cewa Iran din ta kori masu sa ido din baki daya.
Har ila yau, mataimakin ministan harkokin wajen na Iran ya ce; Kasashen turai ba su da hakkin da za su zargi Iran da jefa matakan diplomasiyya cikin hatsari.
Iraqchi ya kuma ce; Iran ta bai wa kasashen na turai dama wadatacciya, amma ba su iya hana Amurka janyewa daga cikin yarjejeniyar ta Nukiliya ba.
Bugu da kari Iraqchi ya ce da Iran tana son bude tattaunawa akan shirinta na makamai masu linzami to da ta yi da gwamantin Turmp. Don haka ba za ta yi ba a wannan lokacin.
342/