ABNA24 : A wani sakon bidiyo da ya gabatarwa taron kolin kungiyar kasashen G5 na yankin Sahel wanda ya gudana a birnin N'Djamena, na kasar Chadi, Mista Guterres ya ce, ya kamata shirin wanzar da zaman lafiya da yaki da ayyukan ta’addanci na Afrika ya dinga samun umarni daga kwamitin sulhun MDD da kuma samun kudaden tafiyar da shirin.
Kungiyar G5 Sahel, ta kumshi kasashen Burkina Faso, Chadi, Mali, Mauritania da jamhuriyar Nijer, kuma kungiyar na taka muhimmiyar rawa wajen shawo kan matsanancin yanayin tabarbarewa tsaro da ayyukan jin kan bil adama a shiyyar.
342/