16 Faburairu 2021 - 11:55
​Dokar Takura Musulmi A Faransa Tana Fuskantar Rashin Amincewa Daga Musulmin Kasar

A kasar Faransa musulmi sun nuna rashin amincewa da dokar da ake shirin kafawa a kasar da sunan yaki da tsatsauran ra’ayi.

ABNA24 : Rahotanni daga kasar faransa na cewa, wasu daga cikin musulmin kasar un gudanar da gangami domin nuna rashin amincewarsu da dokar da ake shirin kafawa a kasar da sunan yaki da tsatsauran ra’ayi wadda ke nufin takura musulmi.

Da dama daga cikin musulmin kasar Faransa suna da imanin cewa, wannan dokar za ta takura su tare da kayyade harkokinsu na addini, da sunan hana yaduwar tsatsauran ra’ayi ko yaki da ta’adanci.

Wasu daga cikin musulmin na Faransa suna bayyana cewa, babban abin da yafi hadari a cikin wannan doka shi ne, tana a matsayin abin da yake halasta keta alfarmar addinin musulunci, tare da bayyana shi a matsayin addinin ta’addanci a hukumance.

Kwamitin musulmin kasar Faransa bai amince da daftarin wannan doka ba, kamar yadda manyan kungiyoyi da cibiyoyin musulmi da dama na kasar ba su amince da hakan ba, amma shugaban kasar Faransa ya kirayi wasu daga limamai ya tilasta su amincewa da samar da wannan doka, amma ba tare da amincewar dukkanin musulmin kasar ba.

342/