ABNA24 : Tsohon jakadan jakadan kasar Amurka a kasar Yemen Gerald Michael Feierstein ya bayyana cewa, kasashen Iran da Saudiyya za su iya taka muhimmiyar rawa wajen kawo karshen yakin kasar Yemen, bisa la’akari da irin tasirin da suke da shi.
Gerald Michael Feierstein ya kasance jakadan Amurka a kasar Yemen a lokacin mulkin Barack Obama, daga bisani kuma ya zama mataimakin sakataren harkokin wajen kasar Amurka a kan harkokin yankin gabas ta tsakiya.
Sannan kuma ya bayyana saka kungiyar Ansarullah ko kuma Alhuthy a cikin jeren kungiyoyin ‘yan ta’adda da gwamnatin Trump ta yi da cewa hakan babban kuskure ne, domin kuwa hakan yana da babbar illa ga rayuwar al’ummar kasar Yemen.
Baya ga haka kuma ya yi ishara da irin matsanancin halin da al’ummar kasar ta Yemen ta shiga, sakamakon yakin da gwamnatin Saudiyya take kaddamarwa kan al’ummar kasar, wanda hakan babu wata riba a cikinsa ga kowa.
Ya jaddada cewa wajibi ne kasashen Saudiyya da Iran su zauna da juna domin warware matsaloli da dama a yankin gabas ta tsakiya, daga cikin har da yakin kasar Yemen da ma wasu batutuwan na daban.
342/