ABNA24 : Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, a daren jiya an ji girgizar kasa a cikin kasar Tajikistan, wadda aka bayyana cewa ta kai ma’aunin ritcher 5.9, wanda kuma lamarin ya auku ne a wani yanki mai tazarar kilo mita 420 a gabashin birnin Doshambe fadar mulkin kasar, a kan iyaka da kasar China, amma duk da hakan an ji motsin kasar a cikin birnin.
Baya ga haka kuma a cikin yankunan arewacin kasashen India da Pakistan an ji motsin kasar a lokacin da lamarin ya faru, sai dai babu wani bayani kan asarar rayuka.
Sai dai wasu rahotanni sun ce a yankin Keshmir na Pakistan wasu shedun gani da ido sun bayyana cewa, wasu bangaye sun zube sakamkon motsin kasar.
342/