6 Faburairu 2021 - 15:08
Gwajin Rokar Dakon Tauraren Dan Adam Da Iran Ta Yi, Ci Gaba Ne Na Ilimi_Hatami

Ministan Tsaron Iran Ya Ce, Kera Makami Mai Linzami Na “Zul-Jihan” Na Dakon Tauraron Dan Adam Da Kasar Ta Yi Ya Sake Tabbatar Da Ci Gabanta Ne Na ilimi.

ABNA24 : Ministan tsaron na Iran Birgediya Janar Amir Hatami wanda yake ziyarar aiki a kasar India ya gana da daliban Iran da suke karatu a can, yana mai cewa; Samarin Iran sun tabbatar da kwazonsu a fagage daban-daban na Iran.

Birgediya janar Amir Hatami ya kuma ce; Makami mai linzamin mai sunan; Zul-Jinah’ na daukar tauraron dan’adam dalili ne akan ci gaban ilimi da Iran din take samu.

Wani sashe na jawabin ministan tsaron na Iran ya bayyana cewa; Juyin juya halin musulunci a karkashin jagorancin Imam Khumaini ( R.A) ya cusawa al’ummar Iran dogaro da kansu, da jin cewa za su iya kutsawa cikin duk wani fage na ci gaba.

342/