ABNA24 : A ranar Asabar ɗin da ta gabata ɗin ne dai wasu majiyoyin labarai na ƙasar Yemen suka bayyana cewar an harba wasu makamai masu linzami daga ƙasar zuwa birnin na Riyadh a matsayin mayar da martani da ci gaba da hare-haren wuce gona da iri da Saudiyya da ƙawayenta suke yi kan al’ummar Yemen.
Rahotannin dai sun bayyana cewar bayan wani lokaci an ji sautin fashewar wasu abubuwa a birnin na Riyadh, duk da cewa wasu majiyoyin labaran ƙasar Saudiyyan sun musanta wannan labarin, to amma dai sun tabbatar da cewa an kai harin kuma makaman kariya na ƙasar sun kakkaɓo wasu daga cikin makamai masu linzamin da aka harbo ɗin.
To sai wasu kafafen watsa labaran yankin sun tabbatar da cewa harin an kai shi ne kan wasu gungun gidajen gidan sarautar Saudiyya ɗin da ke birnin na Riyadh kuma harin ya tarwatsa wajen gaba ɗaya.
Majiyoyin labaran sun ce an kai harin ne daga ɗaya daga cikin sansanonin dakarun gwagwarmaya na ƙasar Yemen ɗin zuwa wannan wajen mai matuƙar muhimmanci a matsayin mayar da martani da hare-haren da Saudiyya da ƙawayen na ta suke kai wa ƙasar ta Yemen.
Wasu majiyoyi sun ce kafafen watsa labaran Saudiyya da ƙawayenta suna ta ƙoƙari wajen ɓoye haƙiƙanin abin da ya faru ne don saboda irin hasarar da aka hasarar da harin ya haifar wa ƙasar ne.
342/