ABNA24 : Harin dai ya auku ne a lokacin da tawagar gwamnatin hadio Mansur mai matsugunni a kasar saudiyya ta iso birnin Aden da ke kudancin Yemen, inda isowar jirgin da ke dauke da su ke dawuya, sai manyan bama-bamai uku suka tarwatse a wurin, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da ashirin wasu da dama kuma suka jikkata.
Gwamnatin Hadi Mansur ta tuhumi kungiyar Ansarullah ko kuma Alhuthi da kai harin, amma kungiyar ta mayar da martani da cewa, su dai nemi wadanda suka kai harin yaka junansu.
Kakakin gwamnatin San’a Shami Daifullah ya bayyana cewa, musayar wuta da aka samu tsakanin jami’an tsaron gwamnatin Hadi da wadanda suke tare da su a filin jirgin, ya kara tabbatar da cewa rikicin na cikin gida ne a tsakaninsu.
Hadi Mansur da ya tsere daga Yemen zuwa birnin Riyad na Saudiyya, inda ya kafa gwamnati a can da ke da matsugunni a cikin manyan otel-otel na birnin Riyad.
342/