ABNA24 : A wata wasika da ya aike wa babban sakataren MDD, da shugaban kwamitin tsaron MDD, na wannan karo Iran za ta bukaci kasashen turan da suka cika alkawuran da suka dauka.
Wakilin Iran, a MDD, ya bayyana cewa matakin da Iran ta dauka na daina aiki da wasu bangarori da yarjejeniyar ta kunsa, ya biyo bayan da Amurka ta sabawa yarjejeniyar.
Game da tsarin musayar na bani-gishiri in baka manda (INTEX), M. Takht-Ravanchi, ya bukaci kasashen turai su nuna da gaske su ke a cikin shekaru biyu masu zuwa.
/342