ABNA24 : Taron dake gudana a Djibouti, na duba halin da ake ciki game da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a kasashen Sudan ta kudu, da Sudan, sai kuma batun rikicin yankin Tigray na Habasha.
Wani batun kuma da taron ke tattaunawa shi ne takkadamar dake tsakanin kasashen Somaliya da Kenya, wanda har ya kai ga shugaban Somalia Mohamed Abdullahi Mohamed, ya sanar da katse huldar diflomatsiya da Kenya, bisa zarginta da shishigi a harkokin cikin gidan kasar da kuma keta hurumin kasar.
342/