1 Disamba 2020 - 10:45
Majalisar “Fatawowin Musulunci” Ta Kasar Rasha Ta Yi Tir Da Kisan Shahid Fakhrizadeh

Shugaban majalisar fatawowin musuluncin na kasar Rasha Sheikh Rufael Eidud-Din ya aike da sako zuwa ga jakadan jamhuriyar musulunci ta Iran dake birnin Moscow Kazim Jalali da a ciki yake yin gaisuwar kisan gillar da aka yi wa Muhsin Fakhrizadeh a ranar juma’ar da ta gabata.

ABNA24 : Shugaban majalisar fatawowin musulunci ta kasar Rasha ya ce; yana isar da sakon gaisuwar ne a madadinsa da kuma dukkanin al’ummar musulmin kasar Rasha zuwa ga jamhuriyar musulunci ta Iran.

A ranar juma’ar da ta gabata ne dai wasu ‘yan ta’adda su ka yi wa shugaban cibiyar nazari da bincike ta ma’aikatar tsaron Iran kwanton bauna, a wani wuri kusa da binin Tehran,inda su ka yi masa kisan gilla.

342/